Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Manyan jami'an tsaro a jihar Kano sun isa cikin ƙaramar fada da ke Kofar Kudd inda tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki yanzu haka.
Kwamishinan ƴan sanda, CP Usaini Gumel, kwamandan sojoji, MA Sadiq, kwamandan hukumar tsaron fararen hula NSCC ML Falala na cikin waɗanda suka gana da Aminu Ado.
Kara karanta wannan
'Muna shirin raka sarki ado bayero fadarsa a kofar kudu,' Tsohon Kwamshina
Wannan na zuwa yayin da lamurra ke ƙara dagulewa game da karagar sarkin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, wanda ya koma cikin fadar Ƙofar Kudu da sanyin safiyar ranar Asabar ɗin da muke ciki.
A rahoton jaridar Daily Trust, Sarki Aminu Ado Bayero, wanda Gwamna Abba ya tsige ya dawo cikin birnin Kano a daren jiya Alhamis.
Tsigaggen Sarkin ya koma ƙaramar fadar Ƙofar Kudd tare da tsattsauran matakan tsaron da ke tare da shi.
Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a kamo Aminu Ado Bayero bisa zargin yunƙurin ta da tarzoma da kuma ruguza tsaron jihar Kano.
Jim kaɗan bayan haka ne jami'an tsaron suka bayyana cewa ba zamu kama tsohon sarkin ba kamar yadda gwamna ya umarta, cewar The Nation.
Kara karanta wannan
Abubuwa sun caɓe, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Kano
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Mohammed Usain Gumel, ne ya sanar da haka a madadin hukumomin tsaro yayin hira wa manema labarai a hedkwatar ƴan sanda.
A wani rahoton kuma Abubuwa sun fara rincabewa yayin da aka fara zaman dar-dar a Kano bayan matasa sun cika harabar fardar Sarkin Kano da makamai.
Mafi yawan matasan sun haɗa da masu goyon bayan tsohon Sarki, Aminu Ado Bayero da kuma Muhammad Sanusi II.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboFyfZdmqqGtl5avorqMnaqsZZSWeq6tzbKYp2WalrqqedOsmKunXajCr3nDoqmaZZaWsaK%2BjKyYq6OZo3qsrc2oZg%3D%3D