Yanzu Yanzu: Ododo Ya Doke Adeyemi Da Sauransu Wajen Samun Tikitin APC Na Zaben Gwamnan Kogi

  • Ahmed Usman Ododo, tsohon mai binciken kudi na kananan hukumomi a jihar Kogi, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar da kuri'u 78,704
  • An gudanar da zaben fidda dan takarar na APC a ranar Juma'a kuma Hon. Patrick Obahiagbon ne ya sanar da sakamakon zaben a madadin shugaban kwamitin
  • Ododo ya lallasa sauran yan takara shida, ciki harda Smart Adeyemi, sanata mai wakiltan Kogi ta yamma

Kogi - Ahmed Usman Ododo, mai binciken kudin kananan hukumomi a jihar Kogi, ya zama dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar mai zuwa a watan Nuwamba.

An gudanar da zaben fidda gwanin na APC ne ta hanyar wakilai a fadin gudunmomin jihar a ranar Juma'a, 14 ga watan Afrilu, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gaskiya 4 Da Suka Bayyana Game da Gwamna da Aishatu Binani a Zaɓen Jihar Adamawa

Legit.ng ta tattaro cewa Hon. Patrick Obahiagbon, sakataren kwamitin shirya zaben fidda gwani na APC a jihar Kogi shine ya sanar da sakamakon a madadin shugaban kwamitin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Kogi: Yadda Ahmed Usman Ododo ya yi nasara

Ahmed Usman Ododo ya yi nasara a zaben fidda gwanin bayan ya samu jimilar kuri'u 78,704 wajen lallasa sauran yan takara shida da tazara mai yawan gaske.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran masu neman takarar tikitin da dama ciki harda mataimakin gwamnan jihar, Edward Onoja, da shugaban ma'aikatan Gwamna Yahaya Bello, Mohammed Asuku sun janye daga tseren.

A zaben fidda gwanin, Mohammed Ozigi Salami shine ya zo na biyu da kuri'u 1,506 yayin da Smart Adeyemi, sanata mai wakiltan Kogi ta yamma ya zo na uku da kuri'u 311.

Kara karanta wannan

Zaben Cike Gurbi Na 2023: Jerin Manyan Yan Takara Da Kallo Ke Kansu

“Bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar 14 ga watan Afrilu, 2023, a Kogi, an ayyana Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC na zaben 2023.“Don haka Ahmed Usman-Ododoya zama zababben dan takarar gwamnan APC a zaben gwamna na da za a yi a watan Nuwamban 2023," Obahiagbon ya ce, jaridar Punch ta rahoto.

Yadda cikon zaben gwamnoni ke gudana a Kebbi da Adamawa

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC na gudanar da cikon zaben gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ0fJJtamaxkaPHtnnYmqWzrV2ksbCwzmawmmWUpLimecCdnLKdnZ56pa2MrJiuqpGjwLZ51pqhnqZdqK6uwc1mq6Kjmam2r3nAqZpmppFix6KuxKdkoK%2BRoruiuoykpqChXw%3D%3D